DARBEJIYA TANA MAGANI KAMAR HAKA

       
   
   DARBEJIYA TANA MAGANI KAMAR                                HAKA
 
(1) MURDAWA KO CIWON CIKI: 
   A tafasa ganyenta kwara bakwai (7) a cikin glass biyu na ruwa sai a tafasa ruwan ya koma kamar misalin glass daya  sai a tace da kyau a ajiye ya huce sannan a sha. A nemi waje mai nutsuwa a kwanta dan yana sa ganin juwa ko aji kamar za’ayi amai.

(2) GUDAWA: Idan an ci wani abinci ko abin sha da ya gurbata ciki to sai a tafasa ganyen darbejiya tsiyaye ruwa na farko a sake zuba wani ruwan a tafasa sai a na biyun za’a tarfa zuma kadan sai a sha.

(3)CIWON SUGA:  samu diyan darbejiya misalign rabin gwangwanin madara sai a saka ganyen mangoro fresh kwara uku a tafasa da kyau a misalign kofi daya na ruwa sai a sha da safe bayan an karya.

(4)MALARIA: Za’a iya shan ruwan ganyen darbejiya dai dai kada a sha dayawa a dinga shan kadan kadan saboda kada ayi amai dan ana so ya tsaya a jikin ka dan ya maka aiki. Daga bisani ana iya tafasa ganyen sai ayi wanka dashi ko ayi surace da shi.

(5)WANKIN JINI: Lokuta da dama jinni kan gurbata saboda wasu kwayoyin cuta haka za’a iya iya tsabtace jinni ta hanyar amfani da ganyn darbejiya inda za’a tafasa ganyen kwara bakwai 7 kacal sai a sha wannan zai baiwa jinni damar gudana a yadda ya dace.

  
 IN SHA ALLAHU ZA A IYYA DA CEWA
.

Post a Comment

0 Comments